in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabar Habasha ta gana da Wang Yi
2019-01-04 10:52:58 cri
Jiya Alhamis, shugabar kasar Habasha Sahle-Work Zewde ta gana da mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin waje na kasar mista Wang Yi, a fadar shugaban kasa dake birnin Addis Ababa.

A yayin ganawar tasu, shugaba Zewde ta bayyana cewa, hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasarta, da jarin da kasar Sin ta zuba a kasar Habasha, sun ba da taimako matuka wajen raya tattalin arzikin kasar, da kyautata zaman rayuwar al'umma. Don haka ne ma a cewar ta, gwamnatin kasar Habasha da mutanen kasar suna son kara hadin gwiwar dake tsakaninsu da kasar Sin, kuma suna sa ran karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Haka kuma, ta taya kasar Sin murnar cimma nasarar gudanar da taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, wanda aka yi a binrin Beijing. Tana mai cewa, halartar manyan shugabannin kasashen Afirka taron, da kuma kyawawan sakamakon da aka cimma a yayin taron, dukkansu sun nuna kyakkyawar makoma ta hadin gwiwar Sin da Afirka.

A nasa bangare kuma, Wang Yi ya ce, farfadowar Sin da Habasha, ta nuna ci gaban kasashe masu tasowa, wanda zai ba da gudummawa ga zaman lafiyar kasa da kasa. Haka kuma, ya jaddada cewa, kasar Sin tana mai da hankali sosai kan raya dangantakar dake tsakaninta da kasar Habasha.

A taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka da aka yi a shekarar 2018, shugaba Xi Jinping ya gabatar da "manyan matakai guda takwas", wanda ya ba da jagoranci kan yadda za a raya hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka a nan gaba. Sabo da haka, kasashen biyu za su iya inganta hadin gwiwar dake tsakaninsu bisa sakamakon da aka cimma, a yayin taron kolin FOCAC da aka yi a birnin Beijing, da kuma shawarar "Ziri daya da hanya daya".

Ya ce Sin na fatan kasar Habasha za ta iya ba da gudummawa wajen inganta hadin gwiwar dake tsakanin Sin da daukacin kasashen nahiyar Afirka baki daya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China