in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi ya buga waya ga ministan harkokin wajen kasar Faransa
2018-11-28 11:08:41 cri
A jiya ne ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, wanda ke yi wa shugaba Xi Jinping rakiya a ziyara da yake yi a kasar Spain ya buga wa takwaransa na kasar Faransa Jean-Yves Le Drian wayar tarho bisa gayyatar da aka yi masa.

Wang Yi ya bayyana cewa, shugaba Xi Jinping zai gana da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron yayin da yake halartar taron koli na kungiyar G20 da za a gudanar a birnin Buenos Aires na kasar Argentina, ganawar dake da babbar ma'ana ga raya dangantakar dake tsakanin Sin da Faransa a nan gaba. Sin tana fatan kara yin hadin gwiwa tare da kasar Faransa don tabbatar da samun kyakkyawan sakamako a yayin taron kolin kungiyar G20.

Wang Yi ya jaddada cewa, sauyin yanayi wani babban kalubale ne da kasashen duniya suke fuskanta. Sin tana son hada kai tare da kasar Faransa da nuna alama mai kyau a yayin taron koli na kungiyar G20, da kokarin ganin nasarar gudanar da taron kasashen da suka sanya hannu kan yarjejeniyar tunkarar matsalar sauyin yanayi ta MDD.

A nasa bangare, Le Drian ya bayyana cewa, shugaba Macron yana begen ganawa da shugaba Xi Jinping a birnin Buenos Aires. Don haka ya kamata Faransa da Sin su kara hada kai ta yadda za a samu daidaito a yayin taron koli na kungiyar G20. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China