Memba a majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi, wanda a yanzu haka ke halartar taro karo na farko kan tsarin musanyar al'adu tsakanin manyan jami'an kasashen Sin da Indiya, ya gana da mai bada shawarwari kan harkokin tsaron kasar Indiya, Ajit Kumar Doval a jiya Lahadi.
A yayin ganawar, bangarorin biyu sun yi musanyar ra'ayi game da dangantakar dake tsakanin Sin da Indiya da ma sauran wasu batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya da suka jawo hankalinsu. (Murtala Zhang)