Wang Yi zai fara da ziyarar aiki ne a kasar Habasha, inda kuma zai ziyarci hedkwatar kungiyar AU dake birnin Addis Ababa, sa'an nan ya isa kasashen Burkina Faso, da Gambia da Senegal tsakanin ranekun 2 zuwa 6 ga watan Janairu dake tafe.
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Madam Hua Chunying ta sanar da hakan a yau Juma'a, yayin taron manema labarai da ya gudana a birnin Biejing.
Ta ce ministan yana zabar kasashen Afirka a matsayin yankin da zai fara kaiwa ziyara a duk shekara, kuma ziyarar ta wannan karo, ci gaba ne ga wannan kyakkyawar al'ada, wadda ke shaida irin muhimmanci da Sin ke baiwa hadin gwiwar ta da kasashen nahiyar Afirka.