in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi: Ziyarar Xi za ta sa kaimi kan hada kai tsakanin kasa da kasa
2018-11-21 19:02:12 cri

Tun daga ranar 15 har zuwa ranar 21 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci kwariya-kwaryar taron shugabannin kasashe mambobin kungiyar APEC, tare kuma da kai ziyarar aiki a kasashen Papua New Guinea da Brunei da Philippines, kana ya gana da shugabannin kasashen dake tsibirran tekun Pasifik wadanda suka kulla huldar diplomasiyya da kasar Sin, yanzu ya kusa kammala wannan ziyara, a don haka mamba a majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya yi bayani kan ziyarar ga manema labarai.

Wang Yi ya bayyana cewa, makasudin ziyarar Xi shi ne domin yada manufar gina kyakkyawar makomar bil Adama, tare kuma da karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasarsa da wadannan kasashe, ta yadda za a ciyar da aikin aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya gaba lami lafiya. Ko shakka babu ziyarar tana da ma'ana matuka, ana iya fahimtar ma'anar daga fannoni hudu:

Na farko, nacewa ga manufar bude kofa bisa tushen yin hakuri da juna domin gudanar da hada kai tsakanin kasashen duniya yadda ya kamata.

Wang Yi ya ce, yayin taron APEC, shugaba Xi ya yi bayani kan kalubalen da kasashen duniya ke fuskanta a halin yanzu, haka kuma ya gabatar da shirin kasar Sin na raya tattalin arzikin yankin Asiya da tekun Pasifik da na duniya baki daya, lamarin da ya jawo hankalin mahalarta taron matuka.

Na biyu, kara zurfafa dadadden zumuncin dake tsakanin kasar Sin da kasashen Brunei da kuma Philippines.

Wang ya ce, wannan shi ne karo na farko da Xi ya kai ziyara kasashen biyu, haka kuma shi ne karo na farko da wani shugaban kasar Sin ya sake kai musu ziyara a cikin shekaru 13 da suka gabata, tabbas ziyarar za ta kawo damammakin ci gabar huldar dake tsakanin sassan biyu.

Na uku, kara zurfafa huldar dake tsakanin Sin da kasashen dake tsibirran tekun Pasifik.

A ganawar da suka yi, an lura cewa, sassan biyu suna son hada kai tare domin ciyar da huldar dake tsakaninsu gaba lami lafiya.

Na hudu, ziyarar ta nuna wa kasa da kasa niyyar kasar Sin ta kara bude kofa ga ketare, tare kuma da samar da damammakin ci gaba ga sauran kasashen duniya.

Yayin ziyarar, shugaba Xi ya yi cikakken bayani kan manufar kasarsa kan manufar yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen ketare, lamarin da ya sa kasashen duniya kara nuna imani kan makomar ci gaban kasar Sin.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China