Wang Yi ya bayyana cewa, harkokin jihar Xinjiang harkokin cikin gida ne na kasar Sin. Yana fatan 'yan jarida su rika ba da muhimmanci ga labarin da Sin ta gabatar a hukunce, wato labarin da gwamnatin jihar Xinjiang ta gabatar, bai kamata a rika sauraron labarai maras tushe daga wasu bangarori game da wannan batu ba.
Wang Yi yana fatan 'yan jarida za su fahimta da nuna goyon baya ga kokarin da gwamnatin jihar Xinjiang ta yi wajen yaki da ta'addanci da masu tsattsauran ra'ayi da tabbatar da zaman lafiya a jihar da tsaron jama'ar yankin gaba daya. Kokarin ya yi daidai da manufar yaki da ta'addanci ta kasa da kasa, kuma shi wani muhimmin bangare ne na aikin yaki da ta'addanci a duniya. Musamman jihar ta hada aikin yaki da ta'addanci da aikin magance ta'addanci, kana ana daukar aikin magance ta'addanci da muhimmancin gaske. Idan aka gudanar da aikin magance ta'addanci yadda ya kamata, za a kawar da bullar masu ra'ayin ta'addanci daga tushe, wannan ita ce hanya mafi dacewa wajen yaki da ta'addanci. (Zainab)