in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rasha ta sanya takunkumi kan karin wasu mutane da hukumomin kasar Ukrain
2018-12-26 13:34:46 cri
Firaiministan kasar Rasha Dmitry Medvedev, ya sanya hannu kan wata doka inda aka fadada adadin sunayen mutanen da kasar Ukrain da wasu hukumomi da aka sanyawa takunkumin, in ji gwamnatin kasar.

Moscow za ta kara adadin mutane sama da 200 'yan kasar Ukraine wadanda aka sanyawa takunkumi a cikin jerin sunayen mutane 322 da hukumomi 68 da aka riga aka sanyawa takunkumin, kamar yadda gwamnatin Rashar ta sanar.

"An zartar da hakan ne domin kare moriyar kasar Rasha, kamfanoninta da al'ummar kasar," in ji Medvedev a sakon da ya wallata ta shafinsa na tweeta bayan sanya hannu kan dokar.

A ranar 1 ga watan Nuwamba, kasar Rasha ta wallafa jerin farko na sunayen, inda take neman dan gidan shugaban kasar Ukraine Petro Poroshenko, mai suna Olexiy, da shugaban majalisar dokokin Ukraine Andriy Parubiy, da wasu manyan ministoci da manyan 'yan kasuwar kasar ruwa a jallo.

Dokar, wanda shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bada umarni a watan Oktoba, ta hada da rike wasu kaddarori wadanda ba zallar kudade ba, bisa zargin rashin tsaro da kuma zargin wasu mutanen dake cikin jerin sunayen mutanen da Rashar take neman ruwa a jallo ne suke sarrafa dokiyoyin, inda ta haramta kwashe dokiyoyin daga kasar Rasha.

Dangantaka ta yi tsami ne tsakanin Kiev da Moscow tun a shekarar 2014, game da batun yankin Crimea da ake takaddama kansa, wanda ke yankin gabashin Ukraine. Ita ma kasar ta Ukraine ta sha kakaba jerin takunkumai ga kasar Rashar tun bayan barkewar rikici tsakanin bangarorin biyu. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China