in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Trump ya soke ganawar da ya shirya yi da Putin saboda takaddamar Rasha da Ukraine
2018-11-30 09:38:14 cri
Shugaba Donald Trump na Amurka ya ce, ya soke ganawar da ya shirya yi da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin, saboda rashin daidaita takadddamar da ta kunne kai tsakanin Rasha da Ukraine.

Trump ya wallafa a shafinsa na Tweeter a kan hanyarsa ta zuwa kasar Argentina cewa, ya soke ganawar ce, saboda har yanzu Rasha ba ta saki jiragen ruwan Ukraine da matukansu da ta tsare ba. A don haka ya bukaci dukkan bangarorin da lamarin ya shafa, da su soke ganawar da ya shirya yi da shugaba Vladmir Putin a kasar Argentina.

A ranar Lahadin da ta gabata ce dai, sojojin ruwan Ukraine suka ce, dakarun kasar Rasha sun bude musu wuta tare da kwace jiragen ruwan kasar ta Ukraine a kusa da zirin Kerch, lamarin da ya kai ga jikkatar sojojin ruwan Ukraine guda 6, biyu daga cikinsu na cikin matsanancin hali.

Amma kuma hukumar tsaron kasar Rasha (FSB) ta ce, jiragen ruwan kasar Ukraine guda ukun sun shiga iyakar ruwan Rasha ne ba tare da iznin ba, duk da gargadin da jiragen ruwan hukumar tsaron Rashan dake tekun Bahar Asuwad suka yi musu. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China