Sergej Lavrov ya bayyana cewa, magoya bayan Ukraine daga kasashen yammacin duniya sun shawarci Ukraine ta dauki matakan soja don tada fitina a tsakaninta da Rasha, ta yadda za ta sanarwa duk duniya cewa, Rasha ta fatattaki Ukraine, hakan za ta fuskanci karin takunkumin da aka kakaba mata.
Sergej Lavrov ya kuma jaddada cewa, Rasha ba ta da shirin dakatar da mu'amala da Ukraine, saboda tsamin dangantakar kasashen biyu ba shi da alaka da jama'ar Ukraine, kuma galibin jama'ar Ukraine na son ganin an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali, da raya kyakkyawar dangantaka tare da Rasha. A cewar Lavrov, Rasha ta fi maida hankali kan raya dangantaka tare da jama'ar Ukraine maimakon gwamnatin kasar. (Murtala Zhang)