in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Fashewar iskar gas ya haddasa rasuwar mutane 21 a Rasha
2019-01-03 11:09:59 cri
Ma'aikatar aikin gaggawa ta kasar Rasha ta fidda sanarwa a jiya Laraba cewa, mutane 21 sun rasa rayukansu sakamakon fashewar iskar gas a wani ginin dake birnin Magnitogorsk na jihar Chelyabinskaya dake yammacin kasar Rasha.

Haka kuma, an ce, ya zuwa karfe 2 da rabi na yammacin jiya Laraba, masu ayyukan ceto sun riga sun gano mutane 27 a karkashin burabuzan gini, ciki har da mutane 21 da suka rasu, da kuma mutane 6 da suka ceto. Kuma cikin wadanda suka rasa rayukansu akwai jarirai guda biyu.

Ban da haka kuma, masu aikin ceton suna ci gaba da neman sauran mutane 20 da suka bace.

Bisa labarin da aka samu, an ce, an gina wannan ginin bene mai hawa 10 ne a shekarar 1973, wani sashe na ginin ya rushe gaba daya sakamakon fashewar iskar gas. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China