Mai magana da yawun ma'aikatar Maria Zakharva ce ta yi wannan tsokaci, bayan da sakataren wajen Amurka Mike Pompeo ya gabatar da wancan kira ga Rasha, yayin wani taron manema labarai da ya gudana a birnin Brussels. Mr. Pompeo dai ya ce kasar sa za ta jingine biyayyarta ga yarjejeniyar INF nan da kwanaki 60, muddin dai Rasha ba ta koma aiki da yarjejeniyar yadda ya kamata ba.
A watan Oktoba ma dai shugaban Amurka Donald Trump, ya yi barazanar janyewa daga wannan yarjejeniya, bisa zargin cewa Rasha na kauracewa aiki da ita. To sai dai kuma Rashan ta sha musanta wannan zargi. (Saminu Hassan)