Mr. Lavrov ya bayyana haka ne, bayan taron hadin gwiwar ma'aikatun harkokin wajen kasashen Rasha da Belarus, wanda aka yi a birnin Minsk fadar mulkin kasar Belarus. Ya ce, matakan da kasar Amurka da kungiyar NATO suka dauka, sun tashi hankulan kasashen nahiyar Turai da Asiya, kuma suna kalubalantar yanayin tsaron kasashen Rasha da Belarus, abin da ya sa kasashen biyu sun mai da martanin a karkashin tsarin kasashen kawancen Rasha da Belarus, da na kungiyar CSTO.
A ranar 20 ga watan Oktoba, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar da cewa, kasarsa za ta janye jikinta daga yarjejeniyar INF, sabo da kasar Rasha ta sabawa yarjejeniyar, kana yarjejeniyar ta hana Amurkan damar raya sabbin makamai.
Daga bisani, a ranar 24 ga watan, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya sanar da cewa, kasar Rasha za ta mai da martani ga kasar Amurka, da zarar ta janye jikinta daga wannan yarjejeniya. (Maryam)