Bayanai na cewa, galibin bakin hauren da aka ceto sun fito ne daga kasashen Afirka dake kudu da Hamadar Sahara, kuma an riga an kai su tashoshin jiragen ruwa dake kusa.
Ko da a kwanan baya ma, sojojin tsaron tekun kasar Morocco sun karfafa aikin sintiri a yankin tekun dake arewacin kasar, sakamakon karuwar matsalolin masu satar shigowa a yankin. (Maryam)