Jirgin mai suna Al Boraq, wanda ke gudun kilomita 200 cikin sa'a guda, an kashe sama da dala biliyan biyu ne wajen gina shi. Gwamnatin Morocco ce ta bayar da sama da dala miliyan 600, yayin wasu kamfaofin ketare suke ba da ragowar kason kudaden aiwatar da aikin.
Kasar Faransa ce dai ta ba da rabin kudaden aikin, yayin da kasashen yankin Gulf da suka hada da Saudiyya da Kuwait da Hadaddiyar Daular Larabawa suka ba da rancen ragowar kudaden.
Daga bisani sarki Mohammed da Macron sun shiga jirgin daga birnin Tangier dake arewacin kasar zuwa Rabat, babban birnin kasar, tafiyar mintuna 80 maimakon kimanin sa'o'i 4 da ake yi a baya. (Ibrahim)