in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da taron kasa da kasa na 11 game da kaurar mutane da samar da ci gaba a Morocco
2018-12-06 10:11:56 cri
An kaddamar da taron kasa da kasa na 11, na karawa juna sani game da kaurar jama'a da samar da ci gaba a kasar Morocco.

An dai bude taron mai lakabin GFMD ne a ranar Laraba a birnin Marrakech, ya kuma samu halartar wakilai daga kasashen duniya sama da 100. Taken taron dai shi ne "Cika alkawuran kasa da kasa domin cin gajiyar samar da ci gaba daga tasirin masu kaura".

Taron ya gabatar da damammaki da za a iya amfani da su, wajen warware wasu daga kalubalen da ke shafar masu kaura. Ya kuma kasance wani dandali na share fagen taro irin sa na farko da za a shirya domin masu kaura, wanda kuma ake fatan gudanarwa a birnin na Marrakech tsakanin ranekun 10 zuwa 11 ga watan nan na Disamba.

Taron na yini 3, ya tattara ministoci da jami'ai daga kasashen duniya masu yawa. Mahalartan sa kuma na amfani da damar, wajen fadada fahimtar su, da hadin gwiwa, game da alaka tsakanin kaurar jama'a da batun ci gaba.

Taron na GFMD wanda kasashen Morocco da Jamus suka yi hadin gwiwar shiryawa, taro ne na sa kai, wanda ba a hukunce ba, ba shi kuma da alaka da wata kasa, dama ce kuma ga dukkanin mambobin MDD, da ma kasashe 'yan kallo dake da sha'awa su shiga a dama da su a fannin. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China