in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rufe taro karo na 8 na biranen Afrika a Morocco
2018-11-25 16:27:46 cri
An kammala taron kasa da kasa karo na 8, na birane da yankunan Afrika wato Africities, da yammacin jiya Asabar a birnin Marrakech na Morocco.

Taron da aka fara tun ranar Talatar da ta gabata, mai taken "sauyawa zuwa yankuna da birane masu dorewa, nauyin dake wuyan gwamnatocin yankuna da kananan hukumomin Afrika", ya samu mahalarta kusan 7,000.

Daga cikin mahalartan, akwai ministoci da hukumomin yankuna da zababbun jami'ansu da jami'an kananan hukumomin da na hukumomin tsakiya da kungiyoyin al'umma da na 'yan kasuwa da masu tafiyar da harkokin tattalin arziki da masu bincike da masana da kuma hukumomin hadin gwiwa na kasa da kasa.

Taron ya kuma tattauna kan dabaru iri guda da ya kamata a dauka wajen inganta rayuwar al'umma a matakin kananan hukumomi da kuma hanyar ba da gudumuwa ga dunkulewa da wanzar da zaman lafiya da hadin kai a Afrika tun daga tushe.

Har ila yau, ya ba da damar wayar da kai kan sabbin nauye-nauyen dake kan shugabannin nahiyar na samar da dabaru masu dorewa na raya yankuna da biranen Afrika. (Fa'iza Msutapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China