A ranar juma'ar data gabata ne aka sanya hannu kan yarjejeniyar bada rancen a Rabat babban birnin kasar, wanda babban daraktan hukumar samar da lantarki da ruwan sha na kasar, Abderrahim El Hafidi, da wakiliyar bankin AfDB a Morocco, Leila Mokadem suka jagoranci sanya hannu kan yarjejeniyar.
Yarjejeniyar ta kunshi samar da rance kudi euro miliyan 79.33 wanda bankin AfDB ya samar, sai kuma kashi na biyu na euro miliyan 43.36 wanda asusun kasar Sin na AGTF ya samar.
AGTF wani asusu ne dake samar da kudi dala biliyan 2 wanda ke tallafawa ayyukan da AfDB da bankin People's Bank of China suke gudanarwa wajen raya cigaban kasashen Afrika.
Wadannan basukan kudade za su tallafawa shirin kasar Morocco na samar da ruwa, wanda ya kunshi janyo ruwa daga madatsun ruwan kasar daban daban don tacewa. (Ahmad Fagam)