in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Morocco sun ceto masu fasa-kwauri 143 a yankin tekun dake arewacin kasar
2018-10-24 10:50:54 cri
Rundunar sojan kasar Morocco ta sanar a jiya Talata cewa, sojojin tekun kasar sun ceto masu fasa-kwauri 143 a yankin tekun dake arewacin kasar.

Rundunar ta ce sojojin tekun sun gudanar da aikin ceton ga jiragen ruwa hudu, wadanda suka makale cikin yankin teku dake kusa da birnin Nador da birnin Tangier na arewacin kasar, jimilar masu fasa-kwauri 143 ne a cikin wadannan jiragen ruwa hudu.

Haka kuma, jiragen ruwa guda uku daga cikinsu sun nitse sakamakon lalacewar da suka yi bayan aikin ceton da sojojin tekun suka yi.

Rahotanni na cewa, masu fasa-kwauri 143 da sojojin Marocco suka ceto sun fito ne daga kasashen Afirka dake kudu da Hamadar Sahara, kuma an riga an kai mutane 113 daga cikinsu tashar jirgin ruwa ta Nador, inda za a kai sauran tashohin jirgin ruwa mafi kusa da su.

A kwanakin baya ne sojojin tekun kasar Morocco suka karfafa aikin sintiri a yankin tekun dake arewacin kasar sakamakon karuwar harkokin fasa-kwauri a wannan yanki. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China