Cikin kudurin, an bukaci gwamnatin kasar Yemen da dakarun Houthi da su aiwatar da yarjejeniyar yadda ya kamata, an kuma bukaci babban sakataren MDD da ya kafa, kuma ya tura wata tawagar wakilai zuwa kasar Yemen domin sa kaimi ga bangarorin biyu da su aiwatar da yarjejeniyar yadda ya kamata.
Cikin kudurin, an bukaci babban sakataren MDDr ya gabatar da shawara kan yadda za a nuna goyon baya kan aiwatar da wannan yarjejeniya kafin karshen shekarar bana. Sa'an nan, an bukaci babban sakataren MDDr da ya bada rahoto kan yadda ake aiwatar da yarjejeniyar a cikin kowane mako, kuma ya gano ko akwai wani bangare da ya aikata wani abu wanda ya sabawa yarjejeniyar.
Cikin kudurin, an kuma bayyana cewa, masu ba da taimakon jin kai zasu iya shiga kasar Yemen da kuma yin tafiya cikin kasar ba tare da wata matsala ba, kuma za a iya shigar da kayayyakin taimakon jin kai cikin kasar lami lafiya.
Bugu da kari, ya kamata a bude tashoshin jiragen ruwa da kuma hanyoyin mota a kasar, kana a bude filin jirgin sama na birnin Sana ga jiragen 'yan kasuwa a kasar. (Maryam)