Shaidun dake kusa da kasuwar sun fadawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, luguden wutan ya rutsa da mutane da dama, saboda ya faru ne lokacin da mutane suka fi hada-hada a kasuwar da ta cika da mutane da suka je sayayya daga makwabtan kauyuka.
A bangare guda kuma, ana ta kwabza fada tsakanin dakarun kasar dake samun goyon bayan dakarun kawance da Saudiyya ke jagoranta da kuma 'yan tawayen Houthi a larduna daban-daban na kasar.
Tun cikin watan Maris din 2015 ne dakarun kawancen suka shiga yakin kasar Yemen, domin fatattakar 'yan tawayen Houthi da mara baya ga Gwamnatin da kasashen duniya ke marawa baya ta Shugaba Abd-Rabbu Mansour Hadi, wanda 'yan tawayen suka tilastawa gudun hijira.
Kawo yanzu, yakin ya yi sanadin mutuwar 'yan kasar sama da 10,000, galibinsu yara, tare da raba wasu miliyan 3 da gidajensu, al'amarin da ya haifar da daya daga cikin matsalolin jin kai mafi muni a duniya. (Fa'iza Msutapha)