in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta nuna rashin amincewa da duk wani matakin da ka iya lahanta lafiyar al'umma da tsananta rikici
2017-12-22 20:07:47 cri
Kwanan nan, Saudiyya ta sake kakkabo makamai masu linzami da dakarun Houthi suka harba zuwa Riyyad, babban birnin kasar ta Saudiyya.

A game da wannan, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Hua Chunying a taron manema labarai da aka kira yau Jumma'a, ta bayyana cewa, labarin ya jawo hankalin kasar Sin, kuma kullum kasar ta Sin na adawa da duk wani matakin da ka iya iya lahanta lafiyar fararen hula, da kuma tsananta rikici.

Kakakin ta ce, yau sama da shekaru biyu ke nan da ake fama da rikicin soja a kasar Yemen, kuma matakin gaggawa da ake bukata shi ne sassa daban daban su cimma wani shiri da zai kai ga warware matsalar ta hanyar yin shawarwari da juna.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China