in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan wadanda suka rasu sakamakon harin da Saudiyya ke kaddamarwa a Yemen ya kai mutum 52
2018-08-03 09:35:18 cri
Rahotanni daga kasar Yemen na cewa, yawan mutanen da suka rasu, sakamakon harin da dakarun Saudiyya ke kaiwa sassan kasar ya kai mutum 52, baya ga wasu 102 da suka jikkata.

Wata sanarwa daga hukumomin lafiyar kasar, wadda kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu kwafinta ta nuna cewa, ya zuwa ranar Alhamis, hare haren na Saudiyya a yankin Hodeidah mai iyaka da bahar maliya sun haddasa rasuwar mutane 52.

Wuraren da hare haren na baya bayan nan suka shafa, sun hada da harabar asibitin al'umma na al-Thawra, da wata kasufar kifi mai yawan jama'a dake daura da asibitin. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China