Haka kuma, ya jaddada cewa, ya kamata bangarorin da rikicin ya shafa su bi dokar jin kai ta kasa da kasa, domin za a yi bincike da kuma gurfanar da wadanda suka aikata laifuka gaban kuliya. Daga bisani kuma, Mr. Guterres ya ba da shawarar cewa, ya kamata sassa daban daban na kasar Yemen su yi shawarwari domin neman hanyar siyasa, wadda ita ce hanya kadai da za a iya bi wajen warware rikicin kasar, da kuma tabarbarewar yanayin jin kai.
A ranar 7 ga wata, jiragen saman yaki na wasu kasashe dake karkashin jagorancin kasar Saudiya, sun kai hari kan fadar shugaban kasar Yemen dake birnin Sana'a, lamarin da ya haddasa rasuwar mutane a kalla guda 6. Sa'an nan kuma, a ranar 9 ga wata, dakarun kungiyar al-Ḥuthiyyun sun harba makamai masu linzami da dama zuwa kasar Saudiya, domin mai da martani gare ta. (Maryam)