Wata sanarwa da ofishin Shugaban kasar ya fitar jiya, ta ce an sauya jami'ai 4 cikin jami'an Firaministan kasar Ahmed Obeid bin Dagr, ciki har da maye gurbin Ministan harkokin cikin gida Hussein bin Arab da Ahmed bin Ahmed Maisari.
Masu sanya ido na ganin cewa, umarnin Shugaban kasar da ya kai ga korar Gwamnonin Lahj da al-Dhalea ka iya janyo kin amincewa da fusata daga mutanen yankin kudancin kasar, wanda ka iya kawo tashin hankali da rashin tsaro.
Gwamnatin Yemen mai samun goyon kasashen waje da hadin gwiwar dakarun kawance da Saudiyya ke jagoranta, sun shafe sama da shekaru biyu suna yaki da 'yan tawayen Houthi dake samun goyon bayan Iran game da jan ragamar da kasar.
Wata Kididdigar MDD ta nuna cewa, tun bayan da dakarun kawancen ta shiga cikin yakin basasar Yemen, sama da mutane 10,000 galibinsu fararen hula sun mutu, sannan wasu kusan miliyan 3 sun rasa matsugunansu. (Fa'iza Mustapha)