in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tabarbarewar halin jin kai a kasar Yemen ta jawo hankalin kwamitin sulhu na MDD
2018-03-16 16:13:37 cri

Kwamitin sulhu na MDD ya bayar da sanarwar shugaba a jiya Alhamis, inda ya mai da hankali kan tsanantar halin jin kai da kasar Yemen ke ciki, inda ya kalubalanci bangarorin da suke rikici da juna da su shiga yunkurin neman sulhuntawa.

Sanarwar ta ce, a halin yanzu akwai mutane miliyan 22.2 da ke bukatar taimakon jin kai a kasar, adadin da ya karu da miliyan 3.4 bisa na bara. Yunwa, cutar kwalara, gyambon 'yar wuya, da ma karancin abinci masu gina jiki na ci gaba da addabar mutane, lamarin da ya jawo hankalin kwamitin sosai.

Don haka kwamitin ya bukaci bangarori daban daban da abin ya shafa da su sauke nauyin jin kai da ke wuyansu wajen bude dukkan tashohin jiragen ruwa na kasar ta Yemen na dogon lokaci. A sa'i daya kuma kwamitin ya yi kira ga dukkan mambobinsa da su samar da kudin taimako.

Bugu da kari, kwamitin ya kalubalanci bangarorin da ke rikici da su shiga yunkurin neman samun sulhuntawa bisa jagorancin MDD, a kokarin ganin an warware ricikin a siyasance.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China