in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadan Tanzania a kasar Sin ya zargi wasu kafofin watsa labaru na kasashen yammacin duniya da maida gudummawar Sin ga kasashen Afirka a matsayin aiki maras kyau
2018-09-27 15:52:19 cri
A kwanakin baya, wasu kafofin watsa labaru na kasashen yammacin duniya sun bayar da labari dake cewa, hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kasashen Afirka, na kara baiwa kasashen Afirka basussuka, wanda hakan ke kawo illa ga samun bunkasuwa mai dorewa a nahiyar Afirka.

Game da wannan, jakadan kasar Tanzania dake kasar Sin Mbelwa Kairuki ya bayyana a jiya ranar 26 ga wata a nan birnin Beijing cewa, wadannan kafofin watsa labaru, ba su son ganin bunkasuwar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, burin su shi ne maida gudummawar da Sin ke samarwa kasashen Afirka a fannonin tattalin arziki da zamantakewar al'umma a matsayin aiki maras kyau.

Jakada Kairuki ya yi nuni da cewa, batun basussuka da aka samu a wasu kasashen Afirka, batu ne da kasashe masu tasowa suke fuskanta, kuma kasar Sin na samar da gudummawa ga kasashen Afirka ba tare da sharadin siyasa ba, da girmama bukatun kasashen Afirka, da kuma yin kokari wajen inganta karfin kasashen Afirka, na samun bunkasuwa da kansu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China