Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya bayyana a gun taron manema labarun da aka gudanar a yau Laraba 12 ga wata cewa, babban taron MDD ya zartas da kudurori biyu dake shafar nahiyar Afirka, wadanda suka yi daidai da ra'ayin da aka cimma daidaito a gun taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka wato FOCAC da aka gudanar a kwanakin baya. Wannan ya shaida cewa, kasashen duniya sun nuna goyon baya ga tunanin yin hadin gwiwa don moriyar juna da kuma raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama.
Hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka ya dace da moriyar bangarorin biyu, kana ya amsa kiran da kasashen duniya suka yi.
Rahotanni na cewa, babban taron MDD karo na 72 ya zartas da kudurin raya sabuwar dangantakar abokantaka a Afirka da kudurin gano dalilin da ya sa aka samun rikice-rikice a Afirka, wadanda kungiyar kasashe 77 ta mika, inda suka jaddada tunanin yin hadin gwiwa don moriyar juna da kuma raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama. (Zainab)