Masana a kasar Kenya, sun ce tallafin kudin da Kasar Sin ke ba kasashen Afrika, ya taimaka wajen inganta zamantakewa da tattalin arziki, ba wai kara musu nauyin bashi ba.
Masanan wadanda suka halarci wani taron karawa juna sani game da taimakon kasar Sin ga kasashen Afrika, wanda cibiyar nazarin manufofin Afrika dake da mazauni a Nairobin Kenya ta shirya, sun ce bashi da tallafin da kasar Sin ke bayarwa ya tabbatar da dorewar ci gaba a nahiyar ba tare da matsawa masu biyan haraji ba.
Babban jami'in zartarwa na cibiyar Peter Kagwanja, ya ce tallafin da kasar Sin ke ba Afrika bisa abotar dake tsakaninsu, ya taimaka wajen shawo kan kalubalen tattalin arziki kamar fatara da cutuka da rashin ababen more rayuwa da fasaha.
Ya kara da cewa, jarin da Sin ta zuba ya taimaka wajen bunkasar tattalin arziki da samar da guraben aikin yi ga matasan nahiyar.
Har ila yau, Peter Kagwanja, ya ce shawarar Ziri Daya da Hanya Daya na samar da kudaden gina ababen more rayuwa da bude kofar kasuwanci ga nahiyar Afrika. Yana mai cewa kasar Sin ta cike gibin da janyewar tallafi daga kasashen yammacin duniya ta haifar.
Shi kuwa babban Daraktan cibiyar David Owiro, cewa ya yi, tallafin da kasar Sin ke ba Afrika ya mayar da hankali ne kan bangarorin da za su amfanawa al'ummar nahiyar kai tsaye. (Fa'iza Mustapha)