A yayin bikin, babban sakataren kwamitin tsakiyar JKS, shugaban kasa, kana shugaban kwamitin harkokin sojan kasar Sin Xi Jinping zai ba da jawabi.
Haka kuma, a lokacin, babban gidan Rediyo da Talibijin na kasar Sin da shafin intanet na Xinhua News za su watsa labaru game da bikin nan take. Sa'an nan, kafofin watsa labarai ta shafin intanet na People.cn, CCTV.com da na China.com.cn da wasu manyan kafofin watsa labarai ta shafin intanet mallakin kwamitin tsakiya za su watsa labaran bikin. (Maryam)