in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi taron karawa juna sani kan manufar yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje ta Sin a Nijeriya
2018-12-16 16:37:45 cri

A ranar 14 ga wata, cibiyar nazarin harkokin Sin ta Nijeriya ta kira wani taron karawa juna sani mai taken "Cika shekaru 40 da aiwatar da manufar yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje a kasar Sin" a birnin Abuja, fadar mulkin kasa ta Nijeriya. Jakadan kasar Sin dake Nijeriya Zhou Pingjian ya gabatar da jawabi a yayin taron, inda ya yi bayani kan yadda kasar Sin ta aiwatar da wannan manufa a kasar, da fasahohin da ta samu, da kuma irin nasarorin da ta cimma da dai sauransu. Haka kuma masanan kasar Nijeriya sun yi tattaunawa kan ma'anar wannan manufa da kuma tasirin da ta yiwa kasa da kasa.

Tsohon ministan harkokin wajen Nierjiya, kana tsohon jakadan Nijeriya a kasar Sin Ambassada Aminu Bashir Wali, da wasu jami'an ma'aikatar harkokin wajen kasar, da wasu jami'an hukumomin gwamnatin kasar, da kuma wasu masanan cibiyar nazarin harkokin kiyaye zaman lafiya da warware sabani, da na jami'ar Abuja da kuma masanan kwalejin kare kasa da dai sauran masanan jami'o'in Nijeriya, da jakadu na kasashen ketare dake kasar Nijeirya da kuma wakilan wasu kafofin watsa labarai sun halarci wannan taro.

Zhou Pingjian ya bayyana cewa, cikin wadannan shekaru 40 da suka gabata, manufar yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje ta kawo manyan sauye sauye ga kasar Sin, ta kuma samar da babbar nasara a fannin raya kasa, kana zaman rayuwar al'ummar kasar ya samu kyautatuwa kwarai da gaske. Manufar ta bada gudummawa wajen raya kasar Sin, ta kuma bada tallafi ga dukkanin al'ummomin duniya. Manufar yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje ta tabbatar da nasarorin da kasar Sin ta cimma a halin yanzu, kuma za ta bada tabbaci kan makoma mai haske da kasar Sin za ta samu a nan gaba.

Aminu Bashir Wali ya bayyana cewa, kasar Sin ta sami babban ci gaba a fannin tattalin arziki da zamantakewar al'umma cikin shakaru 40 da suka gabata, Sin ta cimma wata nasara wadda babu wata kasa da ta taba cimma irinta, watau bada taimako ga mutane sama da miliyan dari 7 wajen kawar da talauci.

A yayin wannan taro, masana sun nuna yabo matuka kan manyan nasarorin da kasar Sin ta cimma a yayin da take aiwatar da manufar yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje. Sun kuma bayyana cewa, a matsayin kasa mai tasowa mafi girma a duk fadin nahiyar Afirka, ya kamata kasar Nijeriya ta koyi fasahohin kasar Sin wajen neman bunkasuwa, ta yadda za ta nemi wata hanyar neman ci gaba da za ta dace da halin da kasar Nijeriya take ciki. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China