in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yankuna masu duwatsu da hamada na kasar Sin suna raguwa cikin sauri
2018-12-14 09:54:36 cri
Adadin yankunan kasar Sin masu duwatsu da hamada yana cigaba da raguwa cikin sauri sakamakon namijin kokarin da hukumar kare muhallin kasar ke yi.

Daga shekarar 2011 zuwa 2016, yankuna masu duwatsu da hamadar suna raguwa da kashi 3.45 bisa 100 a duk shekara, inda saurin raguwar tasu ya kai kashi 1.27 idan an kwatanta da shekaru 5 da suka gabata, in ji Liu Dongsheng, mataimakin shugaban hukumar kula da gandun daji na kasar Sin, ya bayyana hakan ne a taron manema labarai a ranar Alhamis.

A cewar Liu, ana danganta kyautatuwar muhallin da ake samu bisa kokarin da hukumar ke yi wajen kare gandun daji da cigaba da shuka bishiyoyi masu tarin yawa, matakin da ya ba da gudunmowar kashi 65.5 bisa 100 na magance matsalar kwararowar hamada a kasar ta Sin.

An bayyana wannan sakamako ne bayan wani binciken da aka gudanar karo na 3 game da batun yankuna masu fama da duwatsu da hamada, wanda ya dauki kusan shekara guda da rabi, ya kuma hade daruruwan yankuna a larduna 8 na kasar, ciki har da lardunan Hubei da Guangxi.

Kasancewar kwararowar hamada yana daya daga cikin manyan matsalolin dake tunkarar bil adama, wannan ya sa kasar Sin ta ba da fifiko wajen gangamin yaki da matsalar kwararowar hamadar, kuma ta kasance kasa ta farko a duniya da ta cimma nasarar rage karuwar hamada.

Kasar Sin ta yi alkawarin yin musayar fasahohinta na yaki da kwararowar hamada zuwa sauran kasashe da yankunan duniya wadanda ke kan hanyar "shawarar ziri daya da hanya daya" da kuma yankunan sahara, karkashin wani shiri na samar da kariya daga dunkulallen rairayin hamada wanda ke toshe hanyoyin mota.

Sama da jami'ai da kwararru 100 daga kasashe masu tasowa ne suka samu horo daga kasar Sin a cikin wannan shekarar game da yadda za'a shawo kan matsalar kwararowar hamada. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China