in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta samu daidaituwar jarin waje na FDI cikin watanni 11n farkon wannan shekarar
2018-12-14 10:37:33 cri
Jarin kai tsaye na kasashen waje da kasar Sin ta samu wato (FDI) a takaice ya samu daidaituwa a cikin watannin 11 na farko na wannan shekara, ma'aikatar ciniki ta kasar Sin (MOC), ta sanar da hakan a jiya Alhamis.

Baki daya kimanin sabbin kamfanoni 54,703 ne Sin ta kafa bisa amfani da jarin waje cikin wannan wa'adi, inda aka samu karin kashi 77.5 bisa 100 na makamancin lokacin bara, kamar yadda wata kididdigar ma'aikatar ta MOC ta nuna.

Jarin na FDI tsakanin wata na Janairu zuwa Nuwamba ya kai Yuan biliyan 793.3, inda ya yi kasa da kashi 1.3 bisa 100 na makamancin lokacin bara. Idan an kwatanta da dalar Amurka, jarin na FDI ya kai dala biliyan 121.3, wanda ya karu da kashi 1.1 bisa 100 bisa makamancin lokacin bara.

A watannin 11n farko na wannan shekarar, kimanin yuan biliyan 241 na jarin FDI na Sin aka zuba a fannin masana'antu, wanda ya karu da kashi 16 bisa 100 daga shekarar data gabata. Kudaden da aka zuba a fannin manyan fasahohin masana'antu ya haura da kashi 30.2 bisa 100 zuwa yuan biliyan 78.1.

A cikin wannan wa'adin, shirin gwaji na yankin ciniki marar shinge ya samu bunkasuwar sabbin kamfanoni, inda ya karu da kashi 34.6 bisa 100 idan an kwatanta da makamancin lokacin bara, inda jarin na FDI ya karu da kashi 10.4 bisa 100. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China