Wata kididdigar da aka gudanar a kasar ta nuna cewa, adadin wadanda basu da ayyukan yi a biranen kasar bai wuce kashi 4.8 bisa 100 ba a watan Nuwamba, an samu kasa da digo daya na raguwar marasa ayyukan yi a watan da ya gabata da kuma watan Nuwamban shekarar data gabata, inji Mao Shengyong, kakakin hukumar kididdiga ta kasar, inda ya bayyana hakan a taron manema labaru.
Adadin ya ragu fiye da yadda gwamnatin kasar ta yi hasashe na rage marasa ayyukan yi a yankunan biranen kasar da kashi 5.5 a wannan shekarar. (Ahmad Fagam)