Jiya Alhamis, aka bude bikin nune-nunen al'adun shayi na kasar Sin a cibiyar al'adun kasar Sin dake Nijeriya, za a shafe kwanaki uku ana gudanar da bikin, inda za a gabatar da lacca game da al'adun shayin na kasar Sin, da kuma gudanar da tarukan nune-nunen fasahohin harhada shayi da dai sauransu.
Masu fasahar shayi wadanda suka zo daga lardin Fujian na kasar Sin za su gabatar da jawabai da kuma nuna fasahohin harhada shayi a lokacin bikin, domin kara ilmantar da 'yan kasar Nijeriya game da al'adun shayin kasar Sin. (Maryam)