A cikin jawabinsa, Yang Jiechi, ya bayyana cewa, cikin shekaru 5 da suka gabata, shawarar "Ziri daya da hanya daya" ta samu amincewa daga gamayyar kasa da kasa, kuma wasu kasashen duniya sun cimma ra'ayi daya kan tsara wannan shiri cikin hadin gwiwa, domin raya tattalin arzikin kasa da kasa, da karfafa aikin ciniki cikin 'yanci, da yin hadin gwiwa wajen fuskantar kalubaloli da kuma kyautata tsarin ciniki na kasa da kasa. Kasar Sin tana son yin hadin gwiwa da kasashen duniya wajen neman ci gaba bisa manufofin bude kofa ga waje, da yin hadin gwiwa ba tare da gurbata muhalli ba, kuma tana son inganta tsarin ciniki dake tsakanin kasa da kasa, domin kafa dangantakar ciniki da abokai na kasa da kasa, ta yadda za a sami bunkasuwar tattalin arzikin duniya baki daya.
Haka kuma ya ce, kafa wannan kwamitin bada shawarar ya kasance wani muhimmin sakamakon da aka cimma bisa hadin gwiwar bangarori daban daban, muna fatan bangarorin da abin ya shafa za su bada shawara cikin himma da kwazo domin karfafa hadin gwiwar kasa da kasa bisa shawarar "Ziri daya da hanya daya", da kuma bada shawarwari masu kyau ga taron kolin tattaunawar hadin gwiwar kasa da kasa bisa shawarar "Ziri daya da hanya daya". (Maryam)