in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa da kasashe da hukumomi 86 karkashin shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya"
2017-12-23 12:43:33 cri
Hukumar raya kasa da samar da sauye-sauye ta kasar Sin, ta ce kasashe da hukumomi 86, sun rattaba hannu kan yarjeniyoyin hadin gwiwa 100 da kasar Sin, karkashin shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya".

Shugaban Hukumar He Lifeng ya ce shawarar ta samar da gagarumar nasara a shekarar 2017, ya na mai bada misali da nasarorin da aka samu a fannonin da suka hada da kwarewa da zuba jari da kuma hanyar siliki ta zamani.

Ya ce an samu nasara wajen gina kayakin more rayuwa a Pakistan da fara amfani da layin dogon da ya hada biranen Mombasa da Nairobi, da fara shimfida layin dogon Belgrade zuwa Stara Pazova daga bangaren Hungary da Serbia, da tashar jirgin ruwa na Khalifa a Hadaddiyar Daular Larabawa.

Ya ce kawo yanzu, sama da jiragen kasa na dakon kaya 7,000 ne suka yi zirga-zirga tsakanin kasar Sin da Turai.

Har ila yau, He Lifeng, ya ce a shekarar 2018 mai kamawa, hukumarsa za ta mai da hankali wajen aiwatar da yarjeniyoyi da aka cimma yayin taron shawarar "Ziri daya da hanya daya" domin hada gwiwa da kasashen waje da ya gudana a nan birnin Beijing cikin watan Mayun da ya gabata.

Shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya" da kasar Sin ta gabatar a shekarar 2013, na da nufin inganta cinikayya da samar da hanyoyin sufuri da za su hada nahiyar Asiya da Turai da Afrika a kan tsohuwar hanyar cinikayya ta Siliki don samun ci gaba na bai daya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China