in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An buga littafi mai taken "Bayanan Xi Jinping kan manufofin gudanar da harkokin kasa" a harshen Kazakhstan a birnin Astana
2017-06-06 10:48:49 cri
A jiya Litinin ne, aka yi bikin wallafa wani littafi mai taken "bayanan da Xi Jinping ya yi kan manufofin gudanar da harkokin kasa", littafin da aka wallafa a harshen Kazakhstan a birnin Astana, mataimakin ministan sashin fadakar da jama'a na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin Tuo Zhen, jakadan kasar Sin dake kasar Kazakhstan Zhang Hanhui da kuma mataimakin babban direkta a ofishin shugaban kasar Kazakhstan ne suka halarci bikin, inda suka kuma yi jawabai.

A yayin bikin, Tuo Zhen ya bayyana cewa, littafin mai taken " bayanan Xi Jinping kan manufofin gudanar da harkokin kasa" ya yi bayani kan manufofin bunkasuwar kasar Sin da kuma hanyoyin da take bi, da manufofinta na gida da na waje, wadanda suke nuna sabbin manufofi da ra'ayoyi na shugaba Xi Jinping game da gudanar da ayyukan kasa.

A sa'i daya kuma, an amsa tambayoyin al'ummomin kasa da kasa game da batutuwan kasar Sin dake janyo hankulansu.

Wallafa littafin a kasar Kazakhstan zai bude wata sabuwar kofa ga jama'ar kasar ta yadda za su kara fahimtar kasar Sin, da samar da sabon dandali ga kasashen biyu wajen karfafa musayarsu a ayyukan gudanar da harkokin kasa, lamarin da zai zurfafa dangantakar abokantaka a tsakanin kasar Sin da kasar Kazakhstan.

Kimanin wakilai 200 ne daga bangarorin kasar Sin da kasar Kazakhstan suka halarci bikin. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China