in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shawarar zirin daya da hanya daya za ta tallafawa kasa da kasa
2018-01-30 10:45:57 cri
Kwanan baya ne, firaministan kasar Pakistan ya nuna goyon baya ga kafa shawarar ziri daya da hanya daya, dangane da wannan lamari, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana a yayin taron manema labarai da aka shirya a jiya Litinin cewa, babu shakka, kasar Sin ta gabatar da kiran kafa shawarar ziri daya da hanya daya cikin hadin gwiwa, kuma wannan wata kyakyyawar dama ce da za ta taimakawa kasashen duniya.

Haka kuma, ta ce, kasar Sin ta sha yin bayani gama da shawarar ta ziri daya da hanya daya, kuma ma'anar kafa ta ita ce, karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen duniya a fannin samar da muhimman ababen more rayuwa, da yin mu'amala kan manufofin neman bunkasuwa, ta yadda za a cimma moriyar juna da kuma samun ci gaba tare.

Cikin 'yan shekarun nan, ana aiwatar da manufofin kafa shawarar yanayi mai kyau, da cimma sakamako da dama. An samar da guraben ayyukan yi masu dimbin yawa a kasashen da abin ya shafa, da kuma kyautata yanayin bunkasuwa a kasashen da suke cikin wannan shiri. Lamarin da ya inganta hadin gwiwar yankuna daban daban, da samun karbuwa daga kasashe da dama da kuma al'ummominsu.

Bugu da kari, Madam. Hua ta ce, kasar Sin tana son ci gaba da yin hadin gwiwa da bangarorin da abin ya shafa bisa ka'idojin yin shawarwari, da hadin gwiwa da kuma cimma moriyar juna, domin ciyar da manufofin kafa shawarar, ta yadda a nan gaba za a kara samar da damammaki ga ci gaban kasashen duniya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China