Mr. Li wanda ya bayyana hakan a Alhamis din nan, yayin ganawar sa da ministan harkokin wajen Tunisia Khemaies Jhinaoui wanda ke ziyarar aiki a nan kasar Sin.
Li ya ce ana maraba da shigar Tunisia wannan shawara, ya kuma yi fatan sassan biyu za su zurfafa hadin kai mai ma'ana, musamman karkashin lemar kungiyoyin hadin gwiwa, kamar dandalin Sin da kasashen larabawa, da kuma na Sin da Afirka, ta yadda za a daga dangantakar sassa daban daban zuwa wani sabon matsayi.
A nasa bangare, Mr. Jhinaoui ya ce bangaren Tunisia na da burin shiga wannan shawara ta ziri daya da hanya daya, tare da sauran shirye shirye na hadin gwiwa daga dukkanin sassa.