Ya kara da cewa, babu shakka, kasar Sin ce ta fito da shawarar kafa bankin AIIB, amma bai kamata a ce bankin kasar Sin ne. Ya jaddada cewa, bankin AIIB hukumar ce ta kasa da kasa mai kunshe da mambobi guda 57, ana kuma gudanar da harkokin bankin bisa tsarin kasa da kasa da kuma ka'idojin kafa shi.
Haka zalika, ya ce, an kafa bankin AIIB ne domin ba da gudummawar da ba su shafi raya harkokin da bankin duniya da sauran hukumomin sha'anin kudin kasa da kasa suke gudanarwa. Babu shakka, bankin AIIB yana la'akari da shawarar "Ziri daya da hanya daya", zai kuma zuba jari ga ayyukan da suka shafi shawarar yadda ya kamata, bisa ka'idojin neman dauwamammen ci gaba a fannin sha'anin kudi, kiyaye muhalli da kuma ba da tallafi ga 'yan kasashen da suke goyon bayan wannan shawara. (Maryam)