in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Palastinawa Abbas zai tattauna da kasar Sin game da shawarar "ziri daya da hanya daya"
2017-07-17 10:28:54 cri

Shugaban al'ummar Palastinawa Mahmoud Abbas ya bayyana cewa zai tattauna da kasar Sin domin duba hanyoyin da za su ba shi damar yin hadin gwiwa da Sin domin shiga shirin shawarar "Ziri daya da hanya daya".

Shugaban ya yi wannan tsokaci ne a lokacin zantawa da kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua, gabanin ziyarar tasa zuwa kasar Sin, wanda ake sa ran zai fara tun daga yau 17 zuwa 20 ga watan nan na Yuli.

Wannan shi ne karo na 4 ke nan da shugaba Abbas ke yin ziyara a kasar ta Sin. Mahmoud Abbas yana fatan yin musayar ra'ayoyi da mahukuntan kasar Sin game da batutuwa da suka shafi rikicin gabas ta tsakiya a yayin ziyarar tasa, kana za su daddale game da matakan yaki da ta'addanci da tashe tashen hankula.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China