in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Peoples Daily: Tattalin arikin Sin ya bunkasa yadda ya kamata bisa jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin
2018-02-12 11:18:52 cri

A kwanakin baya ne, jaridar Peoples Daily da ake wallafawa a Nijeriya ta rubuta wani sharhi dake bayani game da bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin a shekarar 2017. A cewar sharhin, tattalin arzikin kasar Sin ya bunkasa yadda ya kamata bisa jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin wadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ke jagoranta. A don haka ya kamata kasashen Afirka su yi koyi da fasahohin tsarin bunkasuwar kasar Sin. Sharhin ya kara da cewa, akwai haske a dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka kana zargin da wasu kafofin watsa labaru na kasar Faransa suka yi cewa, wai kasar Sin tana yiwa kungiyar AU leken asiri karya ce da ba ta da tushe.

Sharhin ya bayyana cewa, shugabannin kasar Sin suna da hangen nesa, kana suna tsara manufofin da suka dace da yanayin da ake ciki a kasar Sin, wadanda suka kawo wa kasar Sin bunkasuwar tattalin arziki da samun wadata tare.

Sharhin ya yi nuni da cewa, bunkasuwar tattalin arzikin Sin tana taimakawa bunkasuwar kasashen Afrka cikin sauri, don haka, sharhin na fatan kasar Sin za ta kara cin gajiyar fasahohin tsara manufofin tattalin arziki da sauransu tare da kasashen Afirka bisa tsarin dandalin tattaunawar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China