Da safiyar jiya Jumma'a ne, kamfanin Huawei dake Nijeriya da ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar, suka gudanar da bikin mika kyautar kayayyaki ga 'yan gudun hijira.
Bikin, ya samu halartar ministan harkokin cikin gida na kasar Abdulrahman Dambazau da Sakatarensa Alh. Muhammadu Maccido, da jakadan Sin a Nijeriya Zhou Pingjian da karamin jakadan Sin mai kula da harkokin cinikiyya a Nijeriya Zhao Linxiang.
Yayin bikin, Abdurrahman Dambazau ya yaba da gudummuwar kayayyakin jin kan da ya ce ya zarce moriyar cinikiyya, inda ya ce, ba da tallafi ga 'yan gudun hijira ba nauyi ne da ke bisa wuyan gwamnatin kasar ita kadai ba, yana mai kira ga kamfanonin kasashen waje da su koyi kamfanin Huawei.
A nasa bangare, Mataimakin manajan kamfanin Huawei dake Abuja babban birnin kasar Zhong Haiying, ya yi bayanin cewa, bayan gama bikin, za a yi jigilar kayayyakin daga ma'aikatar harkokin cikin gidan zuwa ga 'yan gudun hijira dake sansanoninsu a arewa masu gabashin kasar kai tsaye, don rage radadi mawuyacin halin da suke ciki.
Tun a shekarar 2009 ne, yankin arewa maso gabashin Nijeriya ke fama da barazanar kungiyar Boko Haram, wadda ta raba mutane kimanin miliyan 2 da dubu dari 3 da matsugunansu, al'amari da ya sa mutane da dama suka rasa ayyukansu inda suke dogara da gudummawa don rayuwa.
Har ila yau, sanadiyyar rikicin, manoma ba sa iya noma, inda mutanen yankin ke fuskantar rashin abinci. (Zainab)