Shugaban Najeriya ya kaddamar da hanyar mota da kamfanin Sin ya gina a birnin Kano
Jiya Laraba ne, shugaban kasar Muhammadu Buhari na Najeriya ya halarci bikin kaddamar da hanyar mota mai tsawon kilomita 2.1 da kamfanin CCECC na kasar Sin ya gina a birnin Kano dake tarayyar Najeriya, kamfanin CCECC na kasar Sin dai ya kashe watanni 8 yana aikin gina tagwayen hanyar, wadda masu ababan hawa ke amfani da ita wajen fita daga birnin.
A jawabinsa, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya nuna godiya matuka ga kamfanin na CCECC, sabo da ingancin hanyar, wadda kuma ta samu yabo daga mazaunan wurin kwarai da gaske. (Maryam)