A jiya ne karamin ofishin jakadancin kasar Sin dake Lagos a tarayyar Najeriya, ya baiwa 'yan sanda gudummawar baburan sintiri guda 9 da na'urorin sanya daki, a wani mataki na inganta ayyukansu.
Da yake mika kayayyakin, babban jami'i mai kula da karamin ofishin jakadancin Sin dake Lagos Chao Xiaoliang, ya bayyana kudurin kasar Sin na ci gaba da taimakawa shirye-shiryen jami'an tsaro na kare rayuka da dukiyoyin jama'a, kamar yadda suka nuna a wannan lokaci.
Da yake karbar kayayyakin, mataimakin sifeto janar na 'yan sanda mai kula da yankin Lagos Ibrahim Adamu ya ba da tabbacin cewa, za a yi amfani da kayayyakin yadda ya kamata.
Bikin mika kayayyakin ya kuma samu halartar manyan jami'an 'yan sandan Najeriya.(Ibrahim)