Kakakin ya bayyana hakan ne yau Alhamis a nan birnin Beijing, inda ya nuna cewa, yanzu ra'ayin ba da kariya da ware kai na karuwa, hakan ya sa kungiyar WTO ke fuskantar kalubale a fannonin martaba da amfaninta, don haka kasar Sin na goyon bayan yiwa kungiyar kwaskwarima da nufin inganta tsarin cinikayya na bangarori da dama ta yadda zai dace da yanayin da ake ciki.
Baya ga haka, kakakin ya bayyana cewa, ya kamata kasashe mambobin kungiyar su warware matsalolin dake tsakaninsu ta hanyar yin shawarwari, ba tare da tilastawa sauran manbobi don su amince da ra'ayinsa ba. (Bilkisu)