in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Karfin cinikin shige da fice na Sin na shekarar 2018 ya zarta na bara
2018-12-07 11:07:02 cri
Adadin cinikin shige da fice na kasar Sin a shekarar bana ya karu cikin sauri, inda ya zuwa tsakiyar watan Nuwamba, karfin cinikin shige da fice ya riga ya wuce adadin na shekarar da ta wuce.

A yayin da yake tsokaci game da matakan gaba a shekara mai zuwa, kakakin ma'aikatar kasuwancin kasar Sin Gao Geng ya bayyana a jiya Alhamis cewa, kasar Sin za ta dauki karin matakai domin raya cinikin shige da fice yadda ya kamata.

Bisa kididdigar da hukumar kwastan ta yi, an ce, a shekarar 2017, karfin cinikin shige da fice na kasar Sin ya kai kimanin yuan biliyan dubu 28, amma ya zuwa tsakiyar watan Nuwambar bana, adadin ya riga ya wuce na shekarar bara gaba daya, wanda ya karu da kashi 15%.

Yayin taron manema labaran da ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ta kira a jiya Alhamis, Gao Feng ya bayyana cewa, bunkasuwar cinikin shige da fice ta ba da gudummawa, wajen fadada bukatun kasuwannin kasa da kasa, da kuma kara shigowar kayayyaki daga ketare zuwa kasar Sin cikin yanayin zaman karko, lamarin da ya kuma tabbatar da karuwar cinikin shige da fice a kasar Sin a bana.

Sa'an nan, Gao Feng ya kara da cewa, cinikin shige da fice na kasar Sin zai ci gaba da samun bunkasuwa a shekarar 2019 mai zuwa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China