A wajen ganawar tasu, shugaban na kasar Sin ya ce bangaren Sin, na son yin kokari tare da Portugal, wajen kara kyautata huldar dake tsakanin kasashen 2, irin ta hadin gwiwa a fannoni daban daban, musamman ma a fannin manyan tsare-tsare.
A nasa bangare, firaministan kasar Portugal Antonio Costa, ya ce kasarsa tana rungumar manufar bude kofa da hadin gwiwa, gami da ciniki cikin 'yanci, sa'an nan kasar tana son halartar shawarar "Ziri daya da Hanya daya" wadda kasar Sin ta gabatar. (Bello Wang)