in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude bikin baje kolin ciniki a Nairobi
2018-12-06 10:30:44 cri

A jiya Laraba ne aka bude bikin baje kolin ciniki na kasar Sin na shekarar 2018, a cibiyar taron kasa da kasa ta Kenyatta dake birnin Nairobi na kasar Kenya.

Bikin dai na gudana ne bisa hadin gwiwar ofishin kasuwancin lardin Guangdong na kasar Sin, da hukumar kasuwancin yankin Xiaoshan ta birnin Hangzhou, da kungiyar raya ciniki ta lardin Shanxi. Ya kuma samu halartar kamfanoni guda 101 wadanda suka zo daga lardunan Guangdong, da Zhejiang, da Jiangsu, da Shanxi, da Fujian da dai sauran manyan lardunan ciniki na kasar Sin guda 8.

Fadin wuraren nune-nune ya kai muraba'in mita 3200, inda aka nuna tufafi, da na'urorin wutar lantarki da sauran kayayyakin da suka shafi fannoni daban daban.

A yayin bikin na tsawon kwanaki uku, kamfanonin cinikin kasar Sin za su yi shawarwari da kamfanonin kasar Kenya, domin kafa dandalin ciniki na Sin da Kenya.

Mukaddashin jakada na wucin gadi a ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Kenya Li Xuhang, ya bayyana a yayin bude bikin cewa, cikin shekaru uku da suka gataba, kasar Sin ta ci gaba da zama kasar da ta fi yin ciniki da kasar Kenya, kuma kasar da ta fi zuba jari a kasar Kenya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China