Da yake tsokaci yayin taron, mataimakin sakataren hukumar koli ta ladaftarwa da bincike, kuma shugaban babbar hukumar sanya ido ta kasar Sin Yang Xiaodu, ya yi kira da a kara martaba ikon MDD, na taka rawar gani a fannin yaki da cin hanci da rashawa, da hadin gwiwar kasashen duniya a fannin.
Mr. Yang ya ce akwai bukatar zurfafa ayyukan gudanarwa a mataki na jam'iyya mai mulkin kasar Sin, da kara inganta yaki da cin hanci yadda ya kamata.
Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya aike da rubutaccen sakon fatan alheri ga taron na birnin Beijing, yana mai jaddada kudurin MDD na ci gaba da goyon bayan kasa da kasa a fannin yaki da cin hanci.
Taron dai ya samu halartar wakilai daga kasashe 125, da sauran kungiyoyin kasa da kasa dake aiki a kasar Sin. (Saminu Alhassan)